An sace 'yan Lebanon a Bayelsa

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption 'Yan sanda sun ce sun fara farautar 'yan bindigar.

Wasu 'yan bindiga a jihar Bayelsa da ke kudancin Najeriya sun kashe 'yan sanda biyu sannan suka sace 'yan kasar Lebanon guda biyu.

An ambato ganau da rundunar 'yan sandan jihar na cewa lamarin ya faru ne ranar Laraba a wani waje da ake aikin gine-gine.

Kakakin rundunar, Anisim Butswat, ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na APC cewa 'yan bindigar sun je wurin ne a cikin jirgin ruwa mai gudun-gaske, sannan suka kashe 'yan sandan da ke gadin wurin gine-gine, kana suka sace 'yan Lebanon din.

Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Ogbia, inda aka sace wasu 'yan kasashe waje guda uku a watan Nuwamban da ya gabata.

Rundunar 'yan sandan ta ce ta fara farautar 'yan bindigar da mutanen da suka yi garkuwa da su.