An dage zaman majalisar wakilan Nigeria

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dogara a lokacin da yake shan rantsuwa

Shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya dage zaman majalisar har sai zuwa ranar 21 ga watan Yuli.

Hakan ya biyo bayan fadan da ya kaure a majalisar bayan da aka samu sabanin tsakanin wasu 'yan majalisa game da batun shugabanci.

An soma rikicin ne bayan da bangarorin biyu da ke hamayya da juna a jam'iyyar APC suka kasa cimma matsaya a kan shugabannin da za a nada.

Bayanai sun nuna cewar uwar jam'iyyar APC ta ba da sunayen wadanda za a nada matsayin shugaban masu rinjaye da mataimakinsa, da kuma babban mai tsawatarwa da mataimakinsa a yayin da wasu 'yan jam'iyyar ke adawa da matakin.

An dambace tsakanin 'yan majalisar na APC abin da ya kara nuna rarrabuwar kawunan da ke tsakaninsu.

Tun bayan da aka zabi Yakubu Dogara a matsayin kakakin majalisar ake samun rashin jituwa tsakanin 'yan majalisar saboda zabensa ya saba da matsayin da uwar jam'iyyar APC ta dauka a kan cewar a zabi Femi Gbajabiamila.