Falasdinu ta kai Isra'ila gaban ICC

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban Falastinawa, Mahmood Abbas

Tawagar Falasdinawa ta ziyarci kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, ICC a karon farko domin gabatar da hujjoji kan zargin Isra'ila da aikata laifukan yaki.

Hujjojin na da nasaba da tashin hankalin da aka yi bara a Gaza da kuma batun mamayen da aka yi a gabar yamma da kogin Jordan.

A watan Afrilu, Falasdinawa suka zama mamba a kotun ICC.

A halin yanzu kotun na gudanar da binciken farko kan zargin aikata laifukan yaki a kan bangarorin biyu.

Isra'ila ta ce zargin da Falasdinawa suka gabatar wani yunkuri ne na saka siyasa a harkokin kotun.