Afrika ta Kudu na tunanin ficewa daga ICC

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Zuma ya yi wa Shugaba Al Bashir lale marhabi

Africa ta Kudu ta bayyana cewa za ta sake yin nazari a kan kasancewarta wakiliya da ta amince da kafuwar kotun shari'ar manya-manyan laifuffuka ta duniya watau ICC.

Hakan ya biyo bayan wata baraka ce da ta kunno kai a kan kasa tsare shugaban kasar Sudan, Omar Al-Bashir din da kasar ta yi a lokacin taron koli na kungiyar kasashen Africa.

Kotun manyan laifukan ta ICC tana neman Omar Al-Bashir ne ruwa a jallo a kan tuhumar aikata laifukan yaki da kisan kare-dangi a yankin Darfur, kuma Africa ta kudun ta kyale shi ne ya bar kasar duk kuwa da wani umarni da wata kotu ta bayar na kada a bar shi ya fita daga kasar.

Wani minista a Africa ta kudun, ya ce a zabinta na karshe gwamnatin za ta janye kwata-kwata daga kotun ta ICC.

Haka kuma ya ce an kafa wani kwamitin ministoci, wanda zai tattauna a kan maganar, kuma mai yiwuwa gwamnatinsa ta tayar da maganar a gaban kotun duniya.