Toyota da Nissan za su janye miliyoyin motoci

Hakkin mallakar hoto AFPGetty Images
Image caption Kamfanin Takata zata janye motoci miliyan uku daga kasuwa saboda matsala a jaka mai dauke da iska.

Manyan kamfanonin kirar motoci a Japan, Toyota da Nissan za su janye motoci miliyan uku daga kasuwa saboda matsala a jaka mai dauke da iska, wacce ke kare direba, ko da hatsari ya auku.

Matsalar wannan jakar mai iska (Air Bag) ta janyo mutuwar mutane takwas.

Kamfanin da ke hada jakar iskar a Japan mai suna Takata, ya ba da sanarwar cewa bai san dalilin da ya sa jakkuna suke fashewa ba.

An riga an janye motoci sama da miliyan 30 daga kasuwa a Amurka kadai saboda matsalar rashin ingancin jakar iskar.

Matsalar tana sa iskar cikin jakar ta fashe, yayinda wasu karafuna ke watsuwa daga cikinta.