'Yan adawa za su kauracewa zaben Burundi

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Pierre Nkurunziza

Jam'iyyun adawa a Burundi sun sanar da cewa za su kauracewa zaben majalisa da na shugaban kasa da za'a yi a nan gaba.

Sun ce tsayawa takara a karo na uku da Shugaba Pierre Nkurunziza ya ke so yayi ya sabawa dokokin kasar.

Kuma a cewarsu hakan bijirewa yarjejeniyar zaman lafiya ne da ya kawo karshen yakin basasa da aka dauki tsawon shekaru 13 a na yi a shekarar 2006.

Za'a yi zaben majalisa a ranar Litinin mai zuwa sai kuma na shugaban kasa wanda za'a yi a watan Yuli.

An kashe kusan mutane 70 a makonnin da aka shafe ana zanga-zanga, wanda hakan ya tilastawa mutane kusan dubu 100 tsallakawa zuwa makwabtan kasashe.