Amurka ta amince da auren jinsi guda

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Babbar kotu a Amurka ta yanke hukuncin ba da damar yin auren jinsi guda a kasar.

Babbar kotun Amurka ta yanke hukuncin cewa mutane na da 'yancin yin auren jinsi daya a kasar.

Hukuncin da alkalai biyar cikin tara suka amince, ya ba da damar gudanar da auren jinsi guda a matsayin abin da shari'ar ta amince da shi a jihohi 50 a Amurka.

Babbar kotun ta ce aure hakki ne na kowa, kuma bai dace a hana masoya jinsa daya damar yin haka ba.

Jama'ar da suka yi cirko-cirko a bakin kofar kotun sun yi murnar sakamakon hukuncin.

Shugaba Obama ya bayyana wannan doka a matsayin nasara wurin cimma burin daidaita sahu tsakanin jinsi, wanda kuma zai karfafa jituwa a tsakanin al'umma.

Fiye da rabin jihohin Amurka sun riga sun yi na'am da auren jinsi daya, amma akwai 'yan kasa dayawa da suke adawa da wannan dabi'a.