An kai hari Masallacin 'yan shi'a a Kuwait

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masallacin 'yan shi'a da aka kai hari a Iraki a kwanakin baya

Rahotanni daga Kuwait sun ce an kai hari a wani masallacin 'yan Shi'a da ke babban birnin kasar.

Bayanai sun ce an kai harin ne a masallacin Imam Sadiq da ke lardin gabashin birnin.

Rahotanni sun ce harin ya auku ne a lokacin da mutane ke gab da fara Sallar Juma'a.

Kawo yanzu babu cikakkun bayanai game da adadin wadanda harin ya rutsa da su.

Ba kasafai ake kai hari makamancin wannan ba a kasar Kuwait.

Kawo yanzu babu kungiyar da ta dauki alhakin kai wannan harin.