An kashe mutane 30 a barikin sojin Somalia

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kungiyar Al- Shabab ta dauki alhakin harin kunar bakin wake a barikin sojojin AU na Somalia.

An kashe akalla mutane 30 a wani hari da 'yan bindiga suka kai barikin sojin kungiyar kasashen Afrika watau AU.

Rahotanni na cewa dan kunar bakin wake cikin wata mota ne, ya taho a guje ya rusa kofar shiga barikin, wacce ke kan hanyar da ta hada babban birnin kasar, Mogadishu da kuma birnin Baidoa.

Mayakan Al-Shabab sun yi ikirarin kwace barikin, yayinda su kuma sojojin AU da na Somalia suka musanta, suna cewa sojojinsu na can suna fafatawa da mayakan.

Kungiyar Al-Shabab ta tsananta hare-hare tun farkon watan azumin Ramadana.

Kungiyar Al-Shabab ta dauki alhakin hallaka dubban mutane a Somalia da Kenya.