An ki tsawaita tallafin ceton Girka

Ministocin kudi na kasashen euro Hakkin mallakar hoto n
Image caption Ministocin kudi na kasashen euro

A ranar Talata mai zuwa ce dai wa'adin da aka baiwa Girkar zai cika inda ake sa ran ta biya asusun bada lamuni na duniya IMF Dala biliyan daya da miliyan dari bakwai.

Gwamnatin Girka ta nemi a tsawaita mata wa'adin ne domin samun damar gudanar da kuri'ar raba gardama a karshen makon gobe akan sabon jadawalin tallafin ceton na baya bayan nan.

A taron manema labarai ministan kudin Girkar Yanis Varoufakis yace tsarin masu bada bashin bai gamsar ba wajen karfafa zuba jari da farfado da tattalin arzikin Girka