Za a rufe bankuna a Girka

Hakkin mallakar hoto AFP

Firaministan Girka Alexis Tsipras ya tabbatar da cewa bankuna kasar za su kasance a rufe, za'a kuma kayyade kudin da jama'a za su iya dauka daga banki.

A wani jawabi da ya yi da aka nuna a talabijin, Mista Tsipras bai bayyana tsawon lokacin da bankunan za su kasance a rufe ba.

Sai dai ya yi kira ga jama'a su kwantar da hankalinsu, yana mai tabbatar masu cewa kudaden ajiyar su da albashi da kuma fansho ba za su yi ciwon kai ba.

Yace: "Shawarar da rukunin kasashe masu amfani da kudin euro suka yanke ta kin amincewa da bukatar gwamnatin Girka ta karin wa'adi takaitacce wanda zai baiwa jama'a damar yanke hukunci a kuri'ar raba gardama kan bukatun masu bada lamuni, abu ne da ba'a tsammace shi ba a matsayin nahiyar Turai da har za'a sanya ayar tambaya akan hakkin al'umma a yancin su na kasa da kuma zabi na dimukradiyya."

Jawabin na shi ya biyo bayan shawarar da Babban Bankin Turai ya yanke na kin kara yawan kudi na rancen gaggawa ga kasar ta Girka.

Bankin ya ce zai tsayar da tallafin akan matakin da aka tsayar a ranar Juma'ar da ta wuce.

Matsayin bankin ya biyo bayan kasa cimma daidaito a tattaunawar da aka yi tsakanin Girka da kasashe masu amfani da kudin euro game da yarjejeniyar tallafin ceto wanda zai cika a ranar Talata mai zuwa.

Karin bayani