Girka ba za ta samu karin kudin rance ba

Hakkin mallakar hoto

Babban Bankin Turai ya yanke shawarar kin kara yawan kudi na rancen gaggawa ga kasar Girka.

Bankin ya ce zai tsayar da tallafin akan matakin da aka tsayar a ranar Juma'ar da ta wuce.

Matsayin bankin ya biyo bayan kasa cimma daidaito a tattaunawar da aka yi tsakanin Girka da kasashe masu amfani da kudin euro game da yarjejeniyar tallafin ceto wanda zai cika a ranar Talata mai zuwa.

Wakilin BBC kan tattalin arziki ya ce hakan na nufin bankunan Girka ba za su sami isassun kudade da za su gamsar da masu ajiya ba wadanda suka zaku domin dauke kudinsu daga bankuna.

Mai yiwuwa kuma bankunan ba za su bude ba a gobe Litinin.

Ministan kudin Girka Yanis Varoufakis ya dora laifin akan Tarayyar Turai yana mai cewa Girka ta yi bakin kokarinta domin cimma yarjejeniya.

Yace: "Wannan lokaci ne marar annuri ga Turai. A tunani na, a tuna cewa Girka ta shiga mawuyacin yanayi na tsawon lokaci a tarihin kafuwarta.

"Wannan abin bakin ciki ne ga Tarayyar Turai da muka rattaba shiga cikinta."

Karin bayani