PDP ta caccaki Buhari a kwanaki 30

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Gwamnatin Buhari ta ce ta na gyara ta'asar da aka tafka ne lokacin PDP

A yayin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke cika wata guda cif da fara aiki a ranar Litinin, jam'iyyar adawa ta PDP ta soki sabuwar gwamnatin da jan- kafa da kuma rashin sanin alkiblar kasar.

Jam'iyyar ta ce gwamnatin na bukatar addu'oi daga 'yan Najeriya saboda rashin yin wani katabus.

Sai dai fadar Shugaban kasar ta ce babu wani jan- kafa da gwamnatin ke yi, domin kuwa ta ce gwamnatin na daukar lokacin ta ne domin gyara irin barnar da gwamnatin PDP ta yi a baya.

Wani mai lura da al'amuran siyasa a Nigeria Malan Abdullahi Bayero ya ce ya yi wuri a fara auna gwamnatin Buhari.