Chadi na kama bakin-haure

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hukumomin Chadi sun sha alwashin murkushe 'yan Boko Haram.

Hukumomi a kasar Chadi na bin gida-gida suna gudanar da bincike domin zakulo bakin-haure a kasar.

An dai yi -waje-da kusan mutum 300, galibinsu baki ne daga kasashen yammacin Afrika da kuma 'yan kasar Kamaru.

Kazalika, an cafke wasu mutane sama da sittin da mahukunta a Chadin ke zargin cewa suna da hannu a harin kunar-bakin-waken da ake zargin kungiyar Boko haram da kai wa a kasar, a makwanni biyu da suka wuce.

Bama bamai guda biyu sun tashi a N'Djamena, babban birnin kasar, ranar Litnin da safe inda suka yi sanadiyar mutuwar mutane 11.

Mazauna birnin sun ce bam din farko ya tashi ne da sassafe a unguwar Dinguessou, yayin da bam na biyu ya tashi mintuna shida bayan na farko.

Mazauna birnin da dama sun shaida wa BBC cewa cikin mutanen da suka mutu har da 'yan sanda biyar.