An rufe bankuna a Girka har zuwa mako 1

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Bankin Girka

Gwamnatin Girka ta tabbatar da cewa bankuna a kasar zasu kasance a rufe a cikin wannan makon saboda matakin da babban bankin Tarayyar Turai ya dauka na kin ci gaba da bai wa kasar tallafin kudin kota kwana.

Za a takaita adadin kudin da mutane zasu rika cirewa a na'urar biyan kudade ta bankuna a rana zuwa Yuro 60, sai dai wannan mataki ba zai shafi masu amfani da katin bankunan wasu kasashe ba.

Matakin ya sa Girkan ba zata bude kasuwar hannayen jari ba.

FirayiMinistan kasar Alexis Tsipras ya bukaci jama'a da su kwantar da hankalinsu, inda ya tabbatar da cewa kudaden ajiyar mutane da albashin su da kudaden Fansaho babu abinda zai same su.

Sai sai Mista Tsibras bai bai fadi zuwa yaushe ne bankunan kasar zasu kasance a rufe ba.

Matakin da babban bankin Tarayyar Turan ya dauka ya biyo bayan rugujewar tattaunawa tsakanin Girka da kasashen Tarayyar Turan a game da yunkurin warware sarkakiyar basussukan kasar da wa'adin su zai cika a ranar Talata.