Sojoji sun yi wa mata fyade a Sudan

Hakkin mallakar hoto
Image caption Motar MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta ce sojoji a Sudan ta kudu sun yi wa mata da dama fyade, kuma suka kona su da ransu a gidanjensu.

A wani sabon rahato, hukumar majalisar mai aiki a can ta ce an aikata cin zarafi da dama a lardin Greter Upper Nile, inda ake matsanancin fada tsakanin gwamnatin kasar da dakarun 'yan tawaye.

A wani lamari da ya faru, an saka wata mata ta rike garwashi a hannayenta a wani yunkuri na tirsasa mata bayyana inda dakarun 'yan tawaye suke.

Haka kum Majalisar Dinkin Duniya ta zargi 'yan tawayen da fyade da kisa da kuma daukar yara kanana aiki.

Ya zuwa yanzu dukkanin bangarorin basu mayar da martani akan zargin ba.