CBN ya tsawaita wa'adin yin rajista

Image caption 'Yan Najeriya da dama sun yi tururuwa zuwa bankunan domin yin rajista.

Babban Bankin Najeriya, CBN ya tsawaita wa'adin yin rajista ga masu asusu a bankunan kasar zuwa ranar 31 ga watan Oktoba.

Wata sanarwa da bankin ya fitar ta ce ta dauki matakin ne saboda 'yan kasar da ba su samu damar yin rajistar ba, su je su yi.

A cewar sanarwar, tsawaita wa'adin yin rajistar zai bai wa 'yan Najeriya da ke zaune a kasashen waje -- wadanda kuma ke da asusu a bankin -- damar yin rajista.

Gabanin tsawaita wa'adin yin rajistar, dubban 'yan kasar da ke da asusu a bankuna ne suka kafa dogayen layuka a bankunan a kokarin da suke ke yi na ganin sun yi rajistar kafin karewar wa'adin ranar Talata.

Babban Bankin ya ce ya dauki matakin yin rajistar masu hulda da shi ne domin rage yawaitar zamba-cikin-aminci da kare satar kudin mutane.