Za a yi zaben raba gardama a Girka

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masu zanga zanga a Girka

Firayi ministan Girka Alexis Tsipras bukaci 'yan kasar su mara masa baya wajen kin amincewa da sababbin sharudan da Tarayyar Turai ta sa musu domin fitar da kasar daga kangin bashi.

Mista Tsipras ya ce idan 'yan kasar suka yi watsi da bukatar sake daukar matakan tsuke bakin aljihu, hakan zai taimaka masa sake hawa teburin tattaunawa domin bin hanyoyin da suka dace na warware bashin.

Ya ce idan mutanen Girka suka ki mara masa baya wajen fatali da sharudan tsuke bakin aljihun, abin da zai fi zame masa mafi alheri shi ne ya sauka daga mulki domin su zabi mutumin da zai aiwatar da sabbin matakan.

Dubban jama'ar kasar masu goyon bayan shirin na gwamnati ne suka yi cincirindo a wajen majalisar dokokin kasar da ke birnin Athens.

Ministan kudi na kasar Jamus Wolfgang Schaeuble ya yi Allah wadai da zaben raba gardamar da Girkan za ta gudanar.

Hukumomin da suke kimanta tattalin arziki sun kara yin kasa da matsayin Girka da kuma bankunan ta.