Jirgi maras matuki ya bige mace a Amurka

Image caption Jirgi mara matuki

'Yan sanda a Amurka sun ce mutumin da ake zargi da gwajin wani karamin jirgin sama mara matuki daya kade wata mata har ta fita hayyacin ta, ya mika kansa ga hukuma.

Jirgin ya bugi matar ne a kanta bayan ya rikito a cikin wani gida.

Jami'ai na ci gaba da bincike dangane da lamarin, wanda ya auku ranar Lahadi.

Lamarin shi ne irin shi na baya bayan nan da wani jirgin kai sakonni mara matuki ya raunata wani mutun.

'Yan sandan Seattle suka ce saurayin matar ne ya rike ta lokacin da jirgin ya bige ta, sannan daya daga cikin abokanenta ya mika wa 'yan sanda jirgin da hoton mutumin da suke gani shi yake gwajin jirgin.

Daga baya wani mutun ya tuntubi 'yan sanda a matsayin wanda ya ke da alhakin lamarin.