'An kashe dakaru 50 a Sinai na Masar'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masar ta tura dakaru a yankin Sinai

Mayakan IS masu da'awar kafa kasar musulunci sun kaddamar da manyan hare-hare kan jami'an tsaro a yankin Sinai na kasar Masar.

Sojojin sun ce har yanzu ana ta arangama.

Wasu majiyoyin tsaro a kasar ta Masar sun ce mutane a kalla 50 ne aka hallaka.

Wani ganau kuma ya shaidawa BBC cewa masu rike da makaman na kan titinan garin Sheikh Zuwaid.

Jami'an sojin sun ce an kai wa shingayen binciken ababen hawa ofisoshin 'yan sanda hari.

Wannan shi ne daya daga hari mafi girma da mayakan suka taba kaddamarwa a yankin na Sinai.

Hare-haren da suka kara matsa kaimi kan jami'an tsaro tun bayan da sojoji suka hambarar da gwamnatin shugaba Mohamed Morsi shekaru biyu da suka gabata.

Hakan na zuwa kwana guda bayan da shugaban kasa,r Abdul Fattah Al Sisi ya lashi takobin kafa dokar da za ta gaggauta yanke hukunci kan mayaka masu kaifin ksihin Islama a kasar--bayan da aka hallaka mai gabatar da kara na kasar ranar Litinin.