Babbar jami'a a Toyota ta yi murabus

Hakkin mallakar hoto
Image caption Kamfanin kera motoci a Japan, Toyota.

Kamfanin kera motoci a Japan, Toyota ya bayar da sanarwar cewa babbar ma'aikaciyar kamfanin ta yi murabus.

An kama Julie Hamp, babbar jami'ar yada labarai, a watan baya bisa zargin hannu a safarar miyagun kwayoyi daga Amurka.

Jami'an kwastam sun gano kwayoyin Oxycodone a cikin wani kunshi da aka aiko mata.

Hamp ta ce ita ba ta san ta shigo da wani abin da ya saba wa doka ba, kuma kamfanin Toyota ya ce bata san ta karya doka a wannan lokacin ba.

Bayan ta yi murabus din, Toyota ya kara nanata matsayar sa a kan daidaita sahun launin fata.