'El-Rufai yana nada bare a kan mukamai'

Image caption El Rufai na shan suka da wadanda suka taya shi cin zabe.

Wasu 'yan jam'iyyar APC a jihar Kaduna da ke Najeriya sun yi zargin cewa gwamna Malam Nasir El-Rufai yana nada bare mukamai.

Masu sukar gwamnatin dai na yin hakan ne ganin nadin da gwamnan ya yi wa Hadiza Bala Usman a matsayin shugabar ma'aikata ta gwamna da Muyiwa Adeleke a matsayin mai bayar da shawara na musamman kan watsa labarai.

Kazalika, 'yan jam'iyyar ta APC sun ce gwamnan bai gaya musu cewa zai nada wadanda ba 'yan jihar ba ne a kan mukaman siyasa lokacin da yake yakin neman zabe.

Sai dai a nata martanin, gwamnatin El Rufai' ta ce cancanta ta sa aka nada mutanen a kan mukaman, tana mai cewa baya ga haka, dukkan su a jihar ta Kaduna aka haife su.