Ebola ta sake bulla a Liberia

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Cutar Ebola ta hallaka mutane da dama

Cutar Ebola mai saurin kisa ta sake bulla a kasar Liberia bayan Hukumar lafiya ta duniya, WHO ta ayyana ta a matsayin kasar da ta yi nasarar yakar cutar.

Gwamnatin kasar ta tabbatar da cewa wani matashi mai shekaru 17 ya kamu da cutar, har ta kashe shi, kuma har yanzu ba a gano yadda aka yi wannan saurayi ya kamu da kwayar cutar ba, da kuma wadanda ya yi mu'amala da su.

A yanzu cutar ta kama mutane biyu a kauyen Nedowein inda matashin nan ya rasu.

Hukumomin lafiya sun ce wadanda suka kamu da cutar sun yi ma'amala da matashin ciki hadda wani mai maganin gargajiya.

Cutar Ebola ta hallaka mutane da dama a kasashe Saliyo da Guinea da kuma Liberia.