Amurka za ta bude ofishin jakadanci a Cuba

Hakkin mallakar hoto
Image caption Amurka da Cuba sun dade suna zaman doya da manja

Shugaba Obama ya sanar da shirin Amurka da kasar Cuba na sake bude ofisoshin huddar jakadancinsu ko wannne a manyan biranen kasashen su, shekaru 54 bayan rufe su.

Mr Obama ya ce sake kulla abotarsu da kasar Cuba hanya ce da tafi dacewa wajen karawa Amurka kima da kuma nuna goyon baya ga dimokradiyya da kare hakkin bil adama.

Ita ma gwamnatin kasar Cuba ta ce za ta bude ofishin huddar jakadancinta daga ranar 20 ga watan Yuli.

Sakataren harkokin wajen Amurka,John Kerry wanda yanzu haka ke birnin Vienna ya tabbatar da cewa zai halarci bikin daga tutar a birnin Havana.

''Nan gama cikin wannan bazarar zan yi bulaguro zuwa kasar Cuba don in halarci sake bude ofishin huddar jakadancin Amurka a birnin Havana," in ji Kerry.