Osinbajo ya kai ziyara Maiduguri

Hakkin mallakar hoto Yusuf Shettima
Image caption Osinbajo ya ziyarci Maiduguri a madadin Buhari

Mataimakin shugaban Nigeria, Farfesa Yemi Osinbajo, SAN ya kai ziyara birnin Maiduguri na jihar Borno domin jajinta wa wadanda rikicin Boko Haram ya shafa.

Mataimakin shugaban kasar wanda gwamnan Kashim Shettima ya tarbe shi a filin saukar jiragen sama na Maiduguri, ya ce shugaba Buhari ne ya umurce shi ya kai ziyarar domin duba yadda lamura ke wakana a yaki da kungiyar Boko Haram.

Osinbajo ya kuma ziyarci sansanin wadanda rikicin Boko Haram ya raba da mullansu a Dalori da ke Maiduguri, sannan kuma ya je asibiti duba wadanda suka ji raunuka sakamakon harin bama-baman Boko Haram.

Mataimakin shugaban kasar ya ziyarci fadar Shehun Borno sannan kuma ya tattauna da kwamandojin tsaro a Maiduguri.

Farfesa Osinbajo ya bar Maiduguri ya kama hanyar zuwa Yola inda nan ma rikicin Boko Haram ya hallaka mutane da dama.