Sojojin Faransa na cin zarafin yara a Burkina Faso

Hakkin mallakar hoto AFP

Ma'aikatar Tsaron kasar Faransa tace an dakatar da wasu sojoji biyu game da zarge zargen cin zarafin kananan Yara a kasar Burkina Faso dake Yammacin Afirka

Masu gabatar da kara Faransawa sun bude gudanar da binciken farko game da wannan batu

Wani mai magana da Yawun sojin kasar yace zarge- zargen na zuwa ne da farkon wannan mako, abinda yasa aka dakatar da sojojin biyu nan take

Dama can Sojojin Faransa sha hudu ne ake gudanar da bincike akansu, bayan zarge zargen cin zarafin kananan Yara a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya