BBC za ta rage ma'aikata sama da 1000

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption BBC za ta rage guraben manyan shugabanni da yawan sassan da ake da su.

BBC ta ce za ta rage fiye da ma'aikatanta guda 1000 daga aiki saboda cike gibin da take da shi na sama da $200m.

Yawancin wadanda za su rasa ayyukan su sun hada da kwararru a wasu fannoni da kuma wadanda ayyukansu ba na wajibi ba ne.

Kazalika za a rage guraben manyan shugabannin BBC da kuma yawan sassan da ake da su.

BBC ta ce tana tsammanin ba za ta rika samun kudade masu yawa daga masu daukar nauyinta.

Darekta Janar na BBC, Tony Hall ya ce rage wadannan ma'aikatan zai sa BBC ta yi tsimin fan miliyan 50 a shekara.