An yi titinunan masu keke a Sao Paulo

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sabuwar titin ta tsaga birnin Avenida Paulista, kuma tsawon wannan ya kai kilomita 2.7.

Masu son ganin an bude hanyar keke, sun ce bude hanyar titin keke a wata sananniyar hanyar matafiya a yankin Latin Amurka da ke Sao Paolo a karshen makon nan, ya nuna sauyi a ra'ayoyin jama'a ga ababen hawa.

An gina sabon titin ne a tsakiyar Sao Paulo, da aka shafe da jan layi a Avenida Paulista.

Birnin Sao Paulo na Brazil yana da fiye da motoci miliyan biyar da dubu 600, kuma ya na matukar cunkoson motoci.

Wannan shirin na cikin wani tsari da magajin garin, Fernando Haddad, ya ke goyon baya.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Magajin garin, Fernando Haddad, (shi ne na hudu da hannun dama) ya fito dana titin shi ma.

Mista Haddad ya sha alwashin cewa kafin shekara ta 2016, zai fadada titunan keke a Sao Paulo daga kimanin tsawon kilomita 64.7 (watau mil 40), zuwa kilomita 400.

'Cece-kuce'

Tsarin dai yana tare da cece-kuce.

Masu sukar tsarin suna korafin cewa ba a tsara shi yadda ya kamata ba, kuma ba a nemi shawarar kwararru ba.

Wasu kuma suna jayayyar cewa bukatar hanyar keken bai cancanci kashe kudi da takura jama'a da aka yi ba.

Zancen titunan keke a Sao Paulo na janyo cece-kuce tun shekarar 1975, farkon lokacin da aka gina titin, amma shekaru 15 bayan haka sai aka mai da shi titin motoci.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An san birnin Sao Paolo dama da cunkoson motoci.

Fiye da rabin jama'ar da ke sukar tsarin, sun ce sau daya suke hawa keke a sati, yayinda kaso 13 cikin dari ke cewa ba sa ma amfani da keken.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu tukin keke sunyi maraba da labarin yunkurin kafa sabuwar doka ta hana toshe titunan keke.

A yanzu dai daya daga cikin fitattun tituna a yankin Latin Amurka da aka sani da cunkoson motoci, an gina masa titin keke.