An bi ka'ida wajen nada Amina Zakari — Buhari

Hakkin mallakar hoto inec
Image caption Gabanin nadin nata, Amina Zakari ce mace kadai a cikin kwamishinonin hukumar zaben ta Najeriya.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya musanta zargin da PDP ta yi cewa ya nada Amina Zakari a mukamin shugabar hukumar zaben kasar ne domin cimma wata boyayyiyar manufa.

Wata sanarwa da mai bai wa shugaban kasar shawara kan harkokin watsa labarai, Femi Adesina ya fitar, ya ce babu kanshin gaskiya a zargin, yana mai bukatar PDP ta kauracewa zarge-zarge.

Shugaba Buhari ya ce an nada Amina Zakari a kan mukamin ne saboda cancantar da ta yi da kuma muradinsa na ganin an dama da mata a cikin gwamnatinsa.

Gabanin nadin nata, Amina Zakari ce mace kadai a cikin kwamishinonin hukumar zaben ta Najeriya.

Hajiya Amina 'yar jihar Jigawa ce da ke arewacin kasar, kuma ta yi digirinta na farko ne a fannin hada magunguna na Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria.

An nada ta kan mukamin ne bayan saukar Farfesa Attahiru Jega, wanda shi ne shugaban hukumar daga shekarar 2010 zuwa shekarar 2015.