Shin IS ta samu gindin zama ?

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Abu Bakr al- Baghdadi Shugaban kungiyar IS

IS ta yi kaurin wajen tayar da hankali, amma duk da hakan dubban mutane sun yi tururuwa zuwa yankin da take zaune kuma kungiyoyi da dama sun yi mata mubaya'a.

Shin me ya sa IS ta jawo hankalin mabiyanta?

Daular baya-bayan nan da ta fi yaduwa - ta Ottoman - an soke ta shekaru 90 da suka wuce.

IS ta yi kokarin yin amfani da irin girmamawa da musulmai ke yi wa kalmar "daular" domin isar da sakon ta ga duniya.

Daulolin musulinci, musamman wadanda aka kafa a tsakanin shekarun 632-1258 AD, sun yi wallafe-wallafe da tsara manhajar koyar da addinin musulinci a akasarin kasashen musulmai.

Image caption kudin da kugiyar IS ta buga na amfanin daular ta

Haka lamarin yake a kokarinsu na kwace wurare da karfin soja domin ba su damar shugabanci a kasashen da Musulmi suke na Larabawa da arewacin Afrika da wasu yankunan Asiya da kuma Spain.

Ana rarraba kasidu a makarantu inda za a ki rubuta abubuwan da ba su da dadin ji game da daular, sai a wallafa abubuwa masu dadin ji game da ita a mujallu masu daukar ido.

An samu wadatar kimiyya da al'adu da muhimman gundunmawa ga al'umma a wancan zamanin.

Yara musulmai da dama sun taso suna karatu da koyo da kuma jin abubuwa a kan "shekaru masu tagomashi" na mulkin daular inda suke tunanin a lokacin shi kadai ne zamanin musulinci a tarihi da ake alfahari da shi kuma ana sha'awar koma ma ta.

A fitowarsa ta farko a bainar jam'a bayan da ya kaddamar da daular shugaban IS, Abu bakr al-Baghdadi, ya bukaci musulman duniya da su yi kaura zuwa yankin da ke hannun IS.

Image caption Mujallar kungiyar IS

Ya gaya musu cewar "ku yi takama saboda a yau kuna da daular da ta dawo muku da martaba da iko da hakokki da kuma jagoranci".

Ya yi alkawarin cewar nan da ba da dadewa ba, "Musulmai za su iya shiga ko ina da izzarsu