Wata mota ta rufta kan rufin daki a Durban

Hakkin mallakar hoto ER24
Image caption Babu wanda ya ji rauni a sakamakon hadarin

Wata mota ta kuskure daga kan titi ta yi kuli-kulin kubura ta fada kan rufin wani gida a birnin Durban na Afrika ta Kudu.

Kamfanin kula da ayyukan gaggawa ER24 ya ce direban motar ya hau kan wani tudu ne sannan ya fado kan wani gida a yankin Kwamakhutha.

Mutumin bai samu raunuka sannan wani mutum da yake bacci a kusa da dakin da motar ta fada bai yi ko kwarzane ba, in ji ER24.

Kakakin ER24, Pieter Rossouw ya shaida wa BBC cewa lamarin "Abin al'ajabi ne."

Ana yawan samun hadarin mota a Afrika ta Kudu saboda tukin ganganci da kuma shan barasa.

Hakkin mallakar hoto ER24
Image caption Mutumin da yake daya dakin bai ji ko kwazane ba