Buhari ya yi Allah wadai da Boko Haram

Hakkin mallakar hoto Yusuf Shetimma
Image caption Gabanin kai hare-haren mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, SAN ya kai ziyara Maiduguri domin jajinta wa wadanda rikicin Boko Haram ya shafa.

Shugaba Muhammadu Buhari na Nigeria ya yi Allah wadai kan kashe-kashe da 'yan Boko Haram suka kaddamar a jihar Borno, inda ya bayyana lamarin a matsayin aikin rashin imani.

A wata sanarwa da kakakinsa, Malam Garba Shehu ya fitar, Shugaba Buhari ya ce kashe mutane maza da mata da kananan yara wadanda ba su yi laifin komai ba su 150 abu ne da kowa ya kamata ya yi tur da shi.

Shugaba Buhari ya ce wannan aika-aikar ta kara jaddada bukatar a gaggauta daukar mataki na hadin gwiwa domin kawo karshen ta'addanci a Nigeria da makwabtanta.

Shugaban kasar ya bukaci Musulmi su fito da babbar murya da su yi tur da masu irin wadannan hare-haren da sunan Musulunci kuma 'yan ta'adda su dai na bata sunan addinin.

Hakkin mallakar hoto BOKO HARAM
Image caption 'Yan Boko Haram sun hallaka mutane fiye da 15,000 a tun daga 2009

Buhari ya kuma jajantawa iyalan wadanda 'yan Boko Haram suka hallaka a Kukawa.

A ranar Laraba ne dai 'yan Boko Haram suka hallaka mutane kusan 100 a kauyuka guda uku a karamar hukumar Kukawa bayan da suka jira mutanen suka idar da Sallah.

A ranar Talata kuma a wasu kauyuka biyu a karamar hukumar Monguno 'yan Boko Haram din sun hallaka mutane 48 a cikin dare sannan suka kona gine-gine da dama a kauyukan.

Rahotanni sun ce ko a ranar Juma'a ma wasu wadanda ake kyautata zaton 'ya'yan kungiyar ne sun kai irin wannan hari a kauyen Zabar-Mari da ke karamar hukumar Jere ta jihar Bornon.

Wannan harin shi ne mafi muni da Boko Haram ta kaddamar tun bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya hau kan mulki a watan Mayu.