An yi jimamin mutuwar 'yan Biritaniya 38

Hakkin mallakar hoto b
Image caption Al'ummar Biritaniya ta kadu game hare-haren

Ana gudanar da bukukuwa domin tunawa da kashe 'yan yawon bude ido 38 galibinsu a Biritaniya a wurin shakatawar nan na Tunisia.

Mko guda cif cif kenan, shugabannin Tunisia sun bi sahun 'yan yawon bude ido da kuma jama'ar garin da suka hallara domin nuna alhini a wurin da aka yi kisan a gabar teku na birnin Sousse.

A halin yanzu kuma a Biritaniya, Sarauniya ta jagoranci kasar wajen yin tsit na minti guda.

Mutane a birane da Ofisoshi da wuraren wasanni da dai sauran wurare sun yi tsatstsaye tare da sadda kawunansu kasa.

Kungiyar IS mai da'awar kafa kasar Musulunci ta ce daya daga cikin 'yan bindigarta ne ya yi harbe-harben.

Hukumomin Tunisia sun ce a halin yanzu mutane takwas da ke da alaka ta kai tsaye da dan bindigar Seifeddine Rezgui na a hannun 'yan sanda.

Kuma sun yi ikirarin cewar a halin yanzu a wargaza gungun da ya dauki nauyin Rezgui.