Girka na cikin tsaka mai wuya

Ministan kudin Girka Yanis Varoufakis Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ministan kudin Girka Yanis Varoufakis

Ministan kudin Girka ya gabatar da wani sako na kafewa akan bakarsa na kin bada kai bori ya hau, kwana guda kafin kuri'ar raba gardamar da za'a kada akan sharudan tallafin ceton kasar.

A hira da wata jarida El Mundo ta Spain, Yanis Varoufakis ya zargi masu baiwa kasar bashi da ayyukan ta'addanci.

Yace suna bukatar jama'a su kada kuri'ar amincewa ne domin cigaba da tursasa 'yan kasar Girka.

Ya kara da cewa bankunan Girka za su bude a ranar Talata ko menene sakamakon raba gardamar zai kasance.

Kuri'ar raba gardamar dai ta haifar da rarrabuwar kawunan jama'a a Athens