Karku amince da shirin ceto- Tsipras

Al'ummar kasar Girka Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Al'ummar kasar Girka

Bangarori biyu a Girka sun kammala gangamin su akan batun gudanar da kuri'ar jin ra'ayin jama'ar da za a gudanar dangane da batun ceton Girka.

Yanzu haka dai an hana duk wani gangami na siyasa yayinda ya rage sa'oi 24 a fara kada kuri'ar jin ra'ayin jama'ar.

A cikin jawabin sa na karshe da yayi a jiya Jumma'a, firaministan kasar ta Girka Alexis Tsipras ya kara jaddada bukatar sa ga al'ummar kasar kan su zabi a'a.

Ya ce rashin amincewa da batun ceton kasar, zai bashi damar cimma manufofi masu kyau tare da masu bin kasar bashi.

Firaministan Girka ya ce al'ummar Girka a ranar Lahadi dukkan mu zamu aike da sakon samun kyakkyawar dimokradiyya da kuma samun kima da martaba.