EFCC ba ta nema na - Kwankwaso

Image caption Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano a Najeriya kuma sanata mai-ci, Rabi'u Musa Kwankwaso ya karyata rahotannin da ke cewa hukumar hana zamba ta kasar wato EFCC ta hana shi sakewa sakamakon tuhumar sa da take yi da almundahana da kudaden 'yan fanshon jihar.

Kwankwason ya ce shi bai ci nanin ba saboda haka nanin ba za ta ci shi ba.

Dangane kuma da batun cewa lauyansa ya kai EFCC din kotu domin neman hana hukumar kama shi, sanata Rabi'u Kwankwaso ya ce shi ma haka ya gani a jaridu domin bai umarci kowa ya yi hakan ba.

Ya kuma alakanta al'amarin da kage irin da abokan hamayya.

Rahotanni dai sun cika gari cewa hukumar EFCC ta na neman Sanata Rabi'u Kwankwaso ruwa a jallo abin da ya hana shi sakewa.