An tube babban mai tsaron shugaban Najeriya

Image caption Ofishin hukumar tsaro ta farin kaya DSS

Rahotanni daga Nigeria na cewa sabon shugaban hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS, Lawal Musa Daura ya tube babban mai ba wa shugaban kasa tsaro, Abdurrahman Mani daga aikinsa.

Ba tare da bata lokaci ba, an kuma maye gurbinsa da Lawal Abubakar wanda shi ne mataimakin direktan hukumar ta DSS a jihar Bayelsa, a baya.

Kawo yanzu ba bu wani bayani daga hukumar ko fadar gwamnatin kan dalilin da yasa aka yi wannan canji.

Sai dai rahotanni na cewa al'amarin ba zai rasa nasaba da misayar yawu tsakanin sabon mai kare lafiyar shugaba Buhari, Muhammad Abubakar wanda ya nemi ya canja wa jami'an hukumar ta SSS wurin aiki a fadar gwamnati ba.

A wani hannun kuma, wasu rahotannin ne ke cewa shugaban hukumar ta DSS, Lawal Musa Daura, ya rage wa mai magana da yawun hukumar, Marilyn Ogar, da wasu jami'ai su 40 mukami.

An dai zargi gwamnatin baya da yin zulaken girma ga wasu jami'an hukumar.