'Yan bindiga sun kashe mutane 13 a Zamfara

Image caption A na tunanin adadin mamatan ka'iya karuwa

A Najeriya, wasu 'yan bindiga wadanda ake kyautata zaton barayin shanu ne sun farwa kauyen Ci-gama da ke karamar hukumar Birnin-Magaji a jihar Zamfara, a yammacin jiya Asabar a inda suka kashe mutane 13.

Wani wanda ya shaida al'amarin ya shaida wa BBC cewa 'yan bindigar sun yi wa kauyen shigar farar dango suka kuma bude wuta akan jama'a.

Al'amarin ya jefa mutanen cikin dimuwa, a inda da dama suka tsere domin neman mafaka a garuruwa masu makwabtaka.

Bayanai sun ce adadin wadanda aka kashe ka iya karuwa zuwa wayewar garin yau Lahadi, sakamakon bin da 'yan bindigar suka yi wa wadanda suka tsere din.

Sai dai ba bu bayanin kan cewa maharan sun kwashi shanu ko akasin haka.