Harin bam ya kashe mutane 11 a Bagadaza

Wani harin bam na mota yayi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 11 a inda mabiya shi'a dake Bagadaza babban birnin Iraqi suka fi yawa.

An kai harin ne a yayin da suke buda baki.

Baya ga kai harin a wajen 'yan Shi'ar, an kuma kai wasu hare-haren a wata Kasuwa da kuma garejin motocin bas-bas.

Hakkin mallakar hoto
Image caption Hare-hare a Bagadaza

Ba dai a san ko su wake da alhakin kai hare-haren ba, sai dai hukumomi a Iraqi na dora alhakin kai hare-hare akan 'yan kungiyar IS a Bagadaza.