Dan kunar bakin wake ya kai hari a coci

Hakkin mallakar hoto AP

'Yan sanda a arewa maso gabashin Najeriya sun ce mutane shidda sun rasu a harin da wani dan kunar bakin wake ya kai a wani coci da ke Potiskum a jihar Yobe.

Wani wanda ya ke cikin cocin na Evangelical a Potiskum lokacin da lamarin ya faru ya shaida wa BBC cewa pastor din cocin na daga cikin wadanda suka rasu.

Wannan hari ya zo ne kasa da kwana biyu da wasu 'yan kunar bakin wake suka ta da bama-bamai a jihar Borno, makwabciyar jihar Yoben.

Kwamishinan 'yan sandan jihar ta Yobe Marcus Danladi ya ce a harin na Potiskum dan kunar bakin waken "ya tarwatsa kansa, ya kuma hallaka mutane hudu tare da jikata wata mace guda".

Ita ma matar ta mutu a asibiti -- abin da ya sa yawan wadanda suka mutun ya kai shidda.

Wannan dai shine hari na baya bayan nan a jerin hare-haren bama-bamai da ake dora alhakinsu Potiskumkan 'yan kungiyar Boko Haram.

Kimanin mutane 200 aka kashe a makon da ya wuce.

Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya yi alkawalin murkushe 'yan kungiyar ta Boko Haram.