Dan kunar bakin wake ya tayar da Bam a Coci

Suicide attack Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Potiskum attack

Wani dan kunar bakin wake ya tayar da Bom a wani coci a Potiskum.

Bam din ya hallaka mutane 6 har da shi. cikin wadanda suka mutu da Pastor da wata yarinya karama, wata mace kuma ta jikkata.

Harin ya zo kasa da kwana 2 da wasu 'yan kunar bakin waken suka ta da bama-bamai a Borno makwabciyar jihar Yoben.

Gwammnatin Najeriya na matsa kaimi a yakin da ta keyi da 'yan Boko Haram wadanda ake zargin kai hare-haren.