'Yan sanda na binciken zaben Ekweremadu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sanata Ekweremadu na shan suka daga wajen APC

Rundunar 'yan sanda Nigeria ta ce ta soma gudanar da bincike game da yadda aka zabi, Sanata Ike Ekweremadu na jam'iyyar PDP a matsayin mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria.

Wani dan majalisar dattawa ne ya kai karar Ekweremadu gaban 'yan sanda bisa zargin cewar an sauya wasu dokokin majalisar domin ba da dama ga zaben mataimakin shugaban majalisar dattawan.

Babban jami'in 'yan sandan Nigeria, CSP Abayomi Shogunle ya shaida wa BBC cewa "Wani dan majalisar dattawa ya kai mana koken a kan sauya wasu takardun majalisa ba bisa ka'ida ba. A kan haka ne ya sa muka rubuta wasika zuwa akawun majalisa domin ya taimaka wajen hada mu da wasu shugabannin majalisar dattawa."

A cewar rundunar 'yan sanda ba a riga an sa ranar da za a tattauna da shugabannin majalisar ba a kan batun wannan korafin.

Tun bayan da aka zabi Sanata Ike Ekweremadu na jam'iyyar adawa ta PDP ake ta ce-ce-ku-ce game da sahihancin zaben.