Girka: Turai na sauraron mataki na gaba

Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption Mr Dijsselbloem ya gana da Mr Tsipras na Girka a birnin Athens

Ministocin kudi na Turai sun ce suna sa ran jin sababbin shawarwari daga Girka bayan da ta kada kuri'ar yin watsi da sharuddan ceton da kasashen duniya za su yi mata.

Shugaban ministocin kudi na kasashen dake amfani da kudin Euro, Jeroen Dijsselbloem, ya ce sakamakon kuri'ar raba gardamar ya kara sa ababuwa sun yi wahala.

To amma ya ce har yanzu burin sa ne da kuma na Girka, a bar Girkar ta ci gaba da kasancewa a cikin kasashen masu amfani da kudin Euro.

"Sakamakon kuri'ar raba gardamar dai a fili ya ke, kuma mun yi amince da shi.To amma bai kusantar da mu ga samun maslaha ba," in ji Dijsselbloem.

Shugabannin kasashe masu amfani da kudin Euro dai za su yi wani taron gaggawa a ranar talata domin tattaunawa kan matsalar kasar ta Girka.