An yi jana'izar mutane 48 a Jos

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An kai harin ne lokacin mutane na sauraron Tafsiri

An yi jana'izar mutane kusan hamsin da suka rasa rayukansu a wasu hare-haren bama-bamai da aka kai a birnin Jos da ke Nigeria.

An kai hare-haren ne a wani masallaci, yayin da ake gudanar da Tafsirin Azumin watan Ramadan, da kuma a wani gidan abinci.

Daya daga cikin bam di ya tashi ne a masallacin 'yan taya a lokacin da Sheik Sani Yahaya Jingir, yake gudanar da tafsirin Al'Qur'ani, abin da ya hallaka mutane 21.

Wani mutum ne ya zo masallacin a inda ya zaro bindiga ya bude wuta a kan mutane kafin ya fara jefa gurneti cikin masallacin, sannan bam din ya tarwatse da shi.

Sheik Jingir ya bayyana cewa wannan lamari ya abin kaico ne matuka, kana ya bukaci mahukunta da sauran masu ruwa da tsaki su kara himma wajen kawo karshen ayyukan tarzoma a kasar.

Malamin dai ya sha sukar masu ayyukan tayar da kayar baya a wa’azzukansa.

Kafin tashin bam din a masallacin, sai da wani ya fara tashi a gidan cin abinci da ke kan titin Bauchi a birnin, abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 23.

Wasu da dama da harin ya jikkata suna asibiti ana musu magani.

Hukumar agajin gaggawa ta NEMA ta ce mutane 47 ne suka jikkata a hare-haren guda biyu.

Ana dai danganta irin wadannan hare-hare ga kungiyar Boko Haram wadda ta halaka mutane da dama a jihar Borno cikin makon da ya gabata.

Tuni dai ita ma gwamnatin jihar Filato ta yi Allah wadai da hare-haren, tare da bayyana daukar matakan tasurara tsaro.

Image caption Gidan abincin Hajiya Talatu Shagalinku na cikin wuraren da aka kai hari