Boko Haram: Sojoji sun saki mutane 182

Hakkin mallakar hoto AP

Rundunar Sojin Najeriya ta sake wasu mutane sama da 182 da aka tsare su bisa zargin cewa suna da alaka da kungiyar Boko Haram.

Kakakin Rundunar Sojin Najeriya ta 7, Kanar Tukur Gusau, ya shaida wa BBC cewa an saki mutanen ne saboda sun gamsu cewa ba su da alaka da kungiyar.

Sakin mutanen dai wani bangare na bukukuwan ranar sojoji ta bana.

Mutanen da aka sake sun hada da Maza 100 da kuma mata da kananan yara, kuma an danka su ga hannun gwamnatin jihar Borno don mika su ga iyalansu.

A kwanan nan ne gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi alkawarin cewa za ta gudanar da bincike a kan wani rahoton da kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta fitar da ke zargin cewa kusan mutum 8000 da ake tsare da su suka mutu a hannun sojoji a kasar.