An yi wa 'yan adawa bulala a Sudan

Image caption Al-Bashir ya dade yana shugabancin Sudan

An yi wa wasu manyan 'yan jam'iyar adawar Sudan uku bulala 20 kowanne saboda tayar da zaune tsaye.

Wani kakakin Jam'iyar Sudanese Congress ta ce an same su da laifi ne sannan aka yi masu bulala kafin lauyansu ya isa kotu.

Mutane ukun an kama su ne a cikin watan Afrilu bayan kiran da a kaurace wa zabe.

Shugaba Omar Al- Bashir, wanda ya kasance kan iko tun shekaru 26 da suka wuce ne ya lashe zaben.