El-Rufai ya haramta bara a Kaduna

Hakkin mallakar hoto kaduna govt
Image caption Gwamna El-Rufai ya jajantawa wadanda suka rasu a harin bam na Sabon gari

Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewacin Nijeria ta haramta bara da kuma tallace-tallace a kan tituna.

Sanarwa da Kakakin Gwamnan jihar, Samuel Aruwan ya sanya wa hannu ta ce an dauki matakin saboda dalilan tsaro, kuma mabaracin da aka samu da laifi zai fuskanci fushin hukuma.

Sanarwar ta kuma jaddada cewa har yanzu dokar haramta achaba na aiki a jihar kuma mutane su guji karya ta.

Gwamna Nasir El-Rufai a cikin sanarwar ya bukaci 'yan jihar su lura da abubuwan da ke kusa da su kuma su kai rahoton duk wanda suke zargi da aikita muggan laifuka.

A ranar Talata ne 'yar kunar-bakin-wake ta hallaka mutane kusan 25 tare da raunata wasu 32 a wajen tantance ma'aikata a Sabon-garin Zaria.