Tsipras zai gabatar da sabbin shawarwari

Image caption Firayiminista Alexis Tsipras

Firayi ministan Girka zai gabatar wa shugabannin Tarayyar Turai sabbin shawarwari kan yadda za a kulla sabuwar yarjejeniyar warware rikicin bashin kasar.

Ya zuwa yanzu dai, kwanaki kalilan ne suka rage kudade su kare wa bankunan Girkan gaba daya.

Kasashen Tarayyar Turan za su yi wani taro a Brussels domin tattauna a kan lamarin.

Faransa da Jamus sun bukaci Girkan data gabatar da tsayayyun shawarori domin kare ta daga ficewa daga cikin Tarayyar Turai.

Mista Tsipras yana son duk wata yarjejeniya da za a kulla, da kunshi a yafewa wa kasar wasu basussuukan.

Bankuna a kasar zasu ci gaba da zama a rufe har zuwa ranar Laraba, sannan kuma matakan takaita yawan kudaden da mutane zasu rika cirewa ta na'urar biyan kudade ATM suna nan.