An hallaka mutane 13 a Barkin Ladi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An sha kaddamar da hare-haren kabilanci a jihar Filato

'Yan bindiga sun hallaka mutane a kalla 13 a kauyen Sho na karamar hukumar Barkin Ladi a jihar Filato.

An yi wa mutanen kwanton bauna ne a kan hanyarsu ta zuwa cikin garin Barkin Ladi domin aikin tattance mutane da bankunan kasar ke yi.

Wasu mutanen kuma sun jikkata sakamakon lamarin.

Wadanda aka kashe galibinsu 'yan kabilar Berom ne, kuma suna zargin Fulani da aikata kisan.

'Yan sanda sun tabbatar da harin amma sun ce kawo yanzu ba a san wadanda suka aikata kisan ba.