Lalong na so a dawo da shingayen bincike

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mr Lalong ya bukaci a dawo da shingayen binciken abubuwan hawa ne bayan hare-haren da aka kai a Jos.

Gwamnan jihar Filato da ke Najeriya, Simon Lalong, ya yi kira ga shugaban kasar Muhammadu Buhari ya dawo da shingayen binciken abubuwan hawa da sojoji suka kafa.

Mr Lalong ya bayyana hakan ne bayan hare-haren da aka kai a birni Jos ranar Lahadi, wadanda suka yi sanadiyar mutuwar a kalla mutane 44.

A cewar sa, shingayen binciken abubuwan hawan suna taimakawa wajen gano 'yan ta'adda kafin su kaddamar da hare-hare.

A kwanakin baya ne Shugaba Buhari ya umarci jami'an tsaron kasar su janye shingayen binciken a wuraren da ba sa fama da yawan kai hare-hare.

Birnin na Jos dai ya sha fama da farmakin 'yan ta'adda.